An tuhumi Gascoigne da tambele

paul gascoigne
Image caption A wata mai zuwa ne za a gurfanar da Paul Gascoigne a gaban kotu

An tuhumi tsohon dan wasan Ingila Paul Gascoigne da laifin tambele sakamakon buguwa da giya da kuma rashin da'a a wata tashar jirgin kasa.

Gascoigne mai shekaru 46 an sallamo shi daga gidan kangararru a Amurka a farkon shekarar nan.

A wannan karan an kama shi ne sakamakon wani lamari da da ya faru da shi a watan nan a Stevenage da ke Hertfordshire.

Jami'an 'yan sandan sufuri na Birtaniya sun kuma tuhumi Mr Gascoigne da laifuka biyu na neman fada.

A ranar 5 ga watan Agusta ne za a gurfanar da tsohon dan wasan na Newcastle da Tottenham da kuma Rangers a gaban kotun majistare a Stevenage.

A ranar hudu ga watan nan na Yuli a ka kama Paul Gascoigne a tashar amma daga bisani a ka bada belinsa.