Real Madrid na shirin sayen Bale

gareth bale
Image caption Gareth Bale ya ce zai koma Real Madrid idan ta yi ciniki da Tottenham

Kociyan Tottenham na neman Gareth Bale ya ci gaba da zama a kungiyar.

Yayin da wasu rahotanni ke cewa dan wasan dan Wales yana shirin komawa Real Madrid.

Jaridar Spain ta Marca ta ruwaito cewa tana ganin Real Madrid na shirin kulla yarjejeniyar shekara shida da dan wasan.

Sai dai kuma kociyan Tottenham din Andrea Villas-Boas ya kafe cewa dan wasan mai shekaru 24 ba na sayarwa ba ne.

Kociyan ya ce, ''dan wasan Tottenham ne, yana daga cikin 'yan wasa masu ban sha'awa a duniya a yanzu.

Dan wasa ne da muke fatan zai ci gaba da zama da mu.''

Bale wanda ya ci wa Tottenham kwallaye 26 a kakar wasannin da ta wuce yana da kwantiragi da klub din har zuwa 2016.

A watan mayu wakilin dan wasan Jonathan Barnett ya shedawa wani gidan talabijin na Spaniya dan wasan zai saurari tayin Real Madrid idan suka yi ciniki da Tottenham.

Yanzu Tottenham din tana Hong Kong domin gasar Kofin Asia wadda ta hada daMan City da Sunderland da kuma China ta kudu.

Bale wanda ya samu kyautar dan wasan shekara da ta matashin dan wasa a kakar da ta wuce ba zai yi wasn farko da Sunderland ranar Laraba ba.

Saboda dan raunin da ya ji a lokacin atisaye amma ana sa ran zai shiga wasa na biyu.

Karin bayani