Ana zargin Falcao da karyar shekaru

radamel falcao
Image caption Radamel Falcao na daya daga cikin 'yan wasa bakwai da Monaco ta saya da tsada a bana

Rahotanni sun bayyana Radamel Falcao da Monaco ta saya daga Atletico Madrid a kan fam miliyan 53 ya yi karyar shekarunsa.

Wata tashar talabijin ta kasarsa Colombia ta yi zargin cewa Falcao ya rage shekarunsa daga 29 zuwa 27.

Tashar ta nuna shedar takardun rijistar makarantarsa ta framare wadda ta nuna cewa n haife shi a ranar 10 ga watan Fabrairu na 1984.

Amma kuma a rijistarsa ta Fifa ya nuna cewaan haife shi a ranar 10 ga watan Fabrairu na 1986.

Idan labarin ya tabbata za ta kasance ke nan dan wasa na bakwai da Monaco ta saya da tsada a bana yana kan karshen ganiyarsa.

Maimakon wanda a ke tsammanin zai ci gaba da kasancewa a ganiyarsa na wasu shekaru uku ko fi.

Karin bayani