Constant na AC Milan ya fice daga fili

kevin constant
Image caption Bayan da Constant ya fice daga filin hukumar kwallon Italia ta sanar da gudanar da bincike kai tsaye

Dan wasan AC Milan Kevin Constant ya fice daga fili lokacin wasan sada zumunta da kungiyar Sassoulu ita ma ta gasar serie A ta Italiya.

Dan wasan dan kasar Guinea mai shekaru 26 ya fice daga filin ne bayan ya buga kwallon cikin 'yan kallo cikin fushi saboda cin mutuncin wariyar launin fata da a kai masa.

Constant ya yi koyi da dan wasan Ghana ne na AC Milan din Kevin-Prince Boateng wanda shi ma a watan Janiru ya fice daga fili saboda cin zarafinsa ta nuna wariyar launin fata

Hukumar kula da kwallon kafa ta Italiya ta sanar da gudanar da bincike a kan lamarin ba da wani bata lokaci ba.

A watan Mayu hukumar kwallon kafa ta duniya fifa tasanar da matakanda za ta dauka don magance matsalar wariyar launin fatar da cewa za a rika mayar da kungiyoyi rukunin baya ko a kore su daga gasa.

Karin bayani