Higuain na gab da komawa Napoli

gonzalo higuain
Image caption Higuain ya koma Real Madrid ne daga River Plate a 2006 kuma ya ci kwallaye 107 a shekara bakwai da ya yi

Dan wasan Real Madrid Gonzalo Higuain ya je kasar Italiya domin tantance lafiyarsa a shirin da Napoli ke yi na sayen shi kan fam miliyan 34 da rabi.

A da dai ana danganta dan wasan mai shekaru 25 dan Argentina da komawa Arsenal.

Kociyan Napolin Rafeal Benitez yana son maye gurbin Edinson Cavani ne wanda ya koma Paris St Germain.

Haka shi ma mai tsaron gidan Liverpool Pepe Reina yana Italiyan inda zai koma Napolin a matsayin aro.

Karin bayani