Za a kai NFF ta Najeriya kara

aminu maigari
Image caption Hukumar NFF da Aminu Maigari ke shugabanta ta ce ta hukunta masu laifin ne domin kare martabar kasar

Jami'an wasu kungiyoyin kwallon kafa na Najeriya da Hukumar Kwallon Kasar, NFF, ta haramta wa shiga harkokin wasanni tsawon rayuwarsu kan zargin magudin wasa, sun ce za su yi karar hukumar.

Dama dai hukumar ta NFF ta dakatar da kungiyoyi hudu ne da wasu jami'ai masu ruwa da tsaki a wasu wasanni biyu, inda Plateau United Feeders suka sha kungiyar AKurba ta Nassarawa

kwallaye saba'in da tara ba ko daya.

Yayin da Kungiyar Police Machine ta Adamawa ta doke Buba Yaro FC Warriors da ci sittin da bakwai ba ko daya.

Amma hukumomi ba su yarda da sakamakon ba kuma suka hukunta wadanda abin ya shafa.

To sai dai kuma daya daga cikin wadanda a ka haramta wa shiga wasanni har abada,mai horar da yan-wasan kungiyar Buba Yaro ta Gombe Bala Yayari,ya musanta labarin.

Ya ce sakamakon da ake yayatawa ba daidai ba ne, kuma za su kai hukumar kwallon kafa ta Nijeriya NFF, kara a gaban hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF da Hukumar Kwallon kafa ta

Duniya sabo da NFF din ba ta yi masu adalci ba.

Karin bayani