Kenya: Ana binciken hukumar kwallo

Tutar Kenya
Image caption Ana zargin jami'an hukumar kwallon kafa ta Kenya da karkatar da kudade

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kenya, EACC, tana bincike a kan manyan jami'an hukumar kwallon kafa ta Kenya bisa zargin cewa dubban daruruwan daloli sun yi batan-dabo.

A cewar jami'ai an samo kudin ne daga hukumar kula da kallon kafa ta duniya, wato FIFA, da sauran hukumomi masu bayar da taimako.

Kakakin hukumar ta EACC, Yasin Ayila, ya ce hukumar tasa ta samu bayanan da ke nuna cewa hukumar kwallon kafar ta Kenya, wato FKF, ta karkatar da kudin da yawansu ya kai dala dubu dari hudu da goma, kuma a yanzu haka ana gudanar da bincike.

Ayila ya shaida wa manema labarai cewa, "Mun samu bayanai dangane da kudin, kuma za a binciki komai, ciki har da bayanan asusun banki da rahotannin banki".

Wakilin Lardin Coast a hukumar kwallon kafar, Hussein Terry, ya gabatar da takardu ciki har da bayanan ajiya a banki ga hukumar yakin da cin hancin da ministan wasanni, Hassan Wario, da FIFA da kuma hukumar kwallon kafa ta Afirka, wato CAF.

Wakiliin hukumar kwallon kafar daga Lardin Nyanza, Sammy Sholei, shi ne ya yi wa Terry rakiya lokacin da ya mika takardun. An dakatar da Sholei da Ayila daga hukumar ta kwallon kafa bayan da suka yi kakkausan suka a kanta, ko da yake sun kalubalanci matakin.

Jami'an sun yi ikirarin cewa hukumar ta samu dala dubu dari hudu da goma a asusun ajiyarta na banki wadanda ba a sanya su a cikin rahoton kudadenta ba.

Shugaban hukumar ta FKF, Sam Nyamweya, ya yi watsi da zarge-zargen, yana mai cewa takardun na jabu ne, kuma ba wanda ke da ikon mallakar takardun na asali sai wadanda ke da alhakin sa-hannu a madadin hukumar.

"wadannan takardun da suke ta yamadidi da su ba namu ba ne. Mun tambayi bankinmu su ma kuma sun musanta cewa daga wurinsu takardun suka fito", inji Nyamweya.