Jamus ta dauki kofin Turai

nadine angerer
Image caption Nadine Angerer ta buge fanareti biyu ta baiwa Jamus damar daukar kofin Turai

Jamus ta dauki kofin gasar kwallon kafa ta mata ta kasashen Turai ta 2013 a karo na shida a jere bayan ta yi nasara a kan Norway.

Mai tsaron gidan Jamus din Nadine Angerer ta kade bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida sau biyu.

Hakan ya baiwa Jamus din damar daukan kofin a karo na shida bayan da ta jefa kwallo daya a ragar Norway din.

'Yar wasan Jamus Anja mittag wadda ta shigo wasan daga baya ita ce ta jefa kwallon da ta baiwa kasarta nasara bayan hutun rabin lokaci.

A matakin wasan na rukuni rukuni na gasar da a ka yi a Stockholm babban birnin Sweden, Norway ta yi nasara a kan Jamus.

Jamus ce ke daukan kofin na Turai na gasar ta mata tun 1993 a jere.

Karin bayani