Ba tabbacin kara taya Fabregas

cesc fabregas
Image caption Ba lalle Manchester United ta kara neman sayen Cesc Fabregas ba

Mai horad da 'yan wasan Manchester United David Moyes ya ce yana da kwarin guiwar sayen sabon dan wasa a bazaran nan.

Amma kuma ya ce har yanzu bai yanke shawara ko zai kara taya Cesc Fabregas ba a karo na uku.

Sau biyu dai Barcelona tana watsi da tayin da Manchester United ta yi na sayen Fabgregas mai shekara 26 da cewa ba na sayarwa ba ne.

Moyes ya ce, ''daman ban taba bada tabbacin cewa nasan zamu same shi ba, za mu duba mu ga abin da zamu yi nan gaba.''

Dan wasa daya kacal da Manchester United ta saya a bazaran nan shi ne Guillermo Varela dan Uruguay.

Amma Moyes ya ce yana da kwarin guiwa za su kara.

Sai dai ya ce a hakan ma suna da kwararrun 'yan wasa a kungiyar ta Manchester United.

Moyes ya kuma ce kyaftin din kungiyar Nemanja Vidic zai buga wasan sada zumuntar da za su yi ranar Litinin a Crewe.

Bayan da dan wasan ya warke daga ciwon bayan da ya hana shirangadin wasan Asia.

A kan batun Rooney kuma tsohon dan wasan Man United din Sir Bobby Charlton ya ce ya yi imani dan wasan zai zauna a klub din.

Rooney wanda ya ci wa United kwallaye 197 yana bukatar wasu kwallayen 53 ya wuceCharlton mai shekaru 75.

Wanda ya ci wa Man U kwallaye 249 a matsayin wanda ya fi ci wa klub din kwallaye a tarihi.

Dattijon ya ce '' mu ba zamu yi sakarcin yanke hukuncin gaggawa ba.

Ba na son ganin mun rasa 'yan wasa masu kyau sosai, Rooney kwararren dan wasa ne mai kyau.''

Karin bayani