Christian Benitez ya mutu

christian benitez
Image caption Christian Benitez ya yi fice a gasar cin Kofin Duniya ta 2006 a Jamus

Tsohon dan wasan kungiyar Birmingham Christian Benitez ya mutu yana da shekara 27.

Benitez da ke yi wa kasarsa Ecuador wasa wanda ya ke kungiyar El Jaish Sports Club ta Qatar ya yi kakar wasanni ta 2009-10 a matsayin aro a St Andrew daga Laguna Santos ta Mexico.

Benitez wanda dan Ermen Benitez ne daya daga cikin 'yan wasan da suka fi ci wa Ecuador kwallaye a tarihi, sau 58 yana yi wa kasarsa wasa.

Ya bar Birmingham ya koma Santos Laguna a 2010 bayan da kungiyar ta Ingila ta ki ba shi kwantiragi na dun-dun-dun.

Dan wasan ya buga wa kungiyarsa wasa ranar Lahadi kuma an ce bai yi maganar wani ciwo da ke damunsa ba.

Ba a dai bayyana abin da ya yi sanadin mutuwar tasa ba.

Benitez wanda a ke wa lakabi da Chucho ya ci kwallaye hudu a wasanni 36 da ya yi a Ingila, ya yi suna a gasar Kofin Duniya ta 2006 a Jamus.

Karin bayani