Barcelona ta rasa Thiago Silva

thiago silva
Image caption Barcelona ta ce tana bukatar dan wasan baya kamar Thiago Silva

Thiago Silva wanda Barcelona ke harin saye ya sabunta kwantiraginsa da kungiyar Paris St-Germain ta Faransa.

Dan wasan na baya ya koma kungiyar ta PSG ne a 2012 a kan fam miliyan 36 tsawon shekaru biyar.

Amma kuma yanzu ana ganin ya kara tsawon zamansa a kungiyar da sabon kwantiragin har zuwa shekara ta 2018.

Barcelona na fatan sayen dan wasan mai shekaru 28 dan kasar Brazil amma kuma batun albashinda za a biya shi ya kawo cikas,daga nan kumain kuma PSG ta dakatar da zakarun na Spain daga maganarsa.

Zakarun na La Liga sun ce yanzu dan wasan baya shi ne abin da suka fi mai da hankali a kan sa.

Saboda Carles Puyol mai shekaru 35 ya ji rauni a guiwa a bara har a ka yi masa aiki a watan Maris.

Yayin da sauran 'yan bayan irin su Pique da Adriano Correia da Javier Mascherano ko dai sun ji ciwo ko kuma an dakatar da su a baran.

An kuma danganta Barcelonan da maganar sayen wani dan bayan dan Brazil, David Luiz na Chelsea amma kungiyar ta musanta a watan Yuni lokacin Tito Vilanova.

Amma kuma rahotanni daga Spain yanzu na nuna cewa Barcelonan karkashin jagorancin sabon kociyansu dan Argentina Gerardo Martino na bukatar sayen Luiz.

A watan Janairu na 2011 Luiz ya koma Chelsea daga Benfica a kan kusan fam miliyan 21 da dubu 300.

Kuma a bara ya sanya hannu kan sabon kwantiragi na shekaru biyar.

Karin bayani