Cisse ya gana da malaman musulunci

papiss cisse
Image caption Papiss Cisse ya ce bayan tunanin gaske ya sauya shawara kan sanya rigar wasan

Papiss Cisse na Newcastle ya ce yana son maida hankalinsa gaba daya kan harkar kwallon kafa bayan ya amince ya sanya rigar kungiyar sakamakon tattaunawa da malaman musulunci.

Cisse dan Senegal musulmi ya ki sanya rigar wasan kungiyarsa ne saboda tana dauke da tambarin kamfanin da ke daukar nauyin samar da jesin mai bada rancen kudi wanda yana ta'ammali da kudin ruwa.

Dan wasan ya ki bin tawagar kungiyar rangadin wasan shirin tunkarar kakar wasanni mai zuwa Portugal a kan cewa ba zai tallata kamfanin ba.

Amma kuma daga baya kungiyar da dan wasan suka sasanta, inda ya amince yanzu ya sa rigar.

Cisse mai shekaru 28 ya ce bayan ya tattauna da kungiyarsa da iyalansa da kuma malaman musulunci a makwannin da suka gabata ya yanke shawarar amincewa.

A watan Janairu na 2012 Papiss Cisse ya koma Newcastle daga kungiyar SC freiburg ta Jamus kuma tun a lokacin ya ci kwallaye 26.

Karin bayani