An sauya wurin wasan Ethiopia da Senegal

blatter da hayatou
Image caption Sepp Blatter na Fifa da Issa Hayatou na Caf

Fifa ta dauke muhimmin wasan Ethiopia na neman zuwa gasar Kofin Duniya da za ta je wa Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a watan Satumba zuwa Congo Brazaville.

Hukumar kwallon kafa ta duniyar ta yi hakan ne saboda dalilai na tsaro bayan hambarar da shugaban kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiyan a shekarar nan.

Yanzu an kai wasan na karshe na rukuni na farko wato Group A zuwa Brazaville.

Haka kuma Fifa din ta dauke wasan karshe na rukuni na goma, Group J, wanda Senegal za ta karbi bakuncin Uganda zuwa Morocco.

Hukumar ta sauya wurin wasan wanda ke da matukar muhimmanci ga Senegal saboda haramcin amfani da babban filin wasan kwallon kafa na Senegal da aka sa.

Za a yi dukkanin wasannin biyu ne a ranar bakwai ga watan Satumba.

Dole ne Ethiopia ta yi nasara a wasan ta samu shiga cikin kasashe goma da za a fitar da biyar a cikinsu.

Wadanda za su wakilci Afrika a gasar Kofin Duniyar bayan da aka karbe makin nasarar da ta yi akan Botswana saboda sanya dan wasan da bai cancanta ba a farkon gasar.

Sai dai idan Ethiopian ta yi canjaras ma za ta iya tsallakewa amma hakan ya danganta ga sakamakon Afrika ta Kudu da Botswana da za a yi a rana daya.

Ita ma Senegal za ta san matsayinta ne a wasan da za ta yi da Uganda a Marrakech.

Kawo yanzu Ivory Coast da Masar da Algeria ne kadai suka tsallake zuwa zagayen kasashe goma na neman zuwa gasar Kofin Duniyar a Afrika.

Karin bayani