Man United za ta yi tayin Fabregas na uku

cesc fabregas
Image caption Man United za ta sake tayin Fabregas a sama da farashi mafi girma da ta sayi dan wasa

Har yanzu Manchester United ba ta hakura da neman Cesc Fabregas ba domin kungiyar na shirin tayin sayensa na uku.

A wannan karon na uku za ta taya shi a farashin da zai zarta farashi mafi girma da ta taba sayen dan wasa wato fam miliyan 30.75 da ta sayo Dimitar Berbatov a 2008 daga Tottenham.

Barcelona ta yi watsi da tayi biyu da United din ta yi a kan dan wasan na fam miliyan 25 da kuma na fam miliyan 30 da cewa dan ba na sayarwa ba ne.

Amma kuma duk da hakan kociyan zakarun na Premier David Moyes ya na son Fabregas din.

Idan Manchester United ta kasa samun nasarar shawo kan Barcelona ta sayar mata da Fabregas din a karo na uku, za ta iya karkata kan Marouane Fellaini na Everton ko kuma Luka Modric na Real Madrid.

Karin bayani