Real na tattaunawa akan Bale- Ancelotti

Image caption Gareth Bale

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce kungiyar na tattaunawa domin sayen dan kwallon Tottenham Gareth Bale.

Kalaman na Ancelotti ya biyo bayan rahotanni a kan cewar Real Madrid na shirin sayen dan wasan akan fiye da pan miliyon 80 da yafi abinda aka sayi Cristiano Ronaldo in 2009.

Ancelotti ya shaidawa manema labarai a sansanin horon Real dake Los Angeles: "Na yi amanna kulob din na tattaunawa don warware batun, kuma zamu ga yadda lamarin zai kasance".

Bale ya shaidawa Spurs cewar yanason ya gana da Madrid.

Kawo yanzu a hukumance, Real bata bada tayin Bale.

Ancelotti ya koma Bernabeu ne bayan ya bar Paris St-Germain, kuma yana kokarin sayen karawa tawagar karfi.

Karin bayani