Tottenham za ta sayi Saldado

Image caption Roberto Saldado ya bugawa Spain sau 11

Tottenham Hotspur ta amince da sayen dan wasan Valencia Roberto Soldado akan fam miliyan ashirin da shida.

Zai sanya hannu a yarjejeniyar shekaru hudu, kuma zai kasance dan wasa na uku da Spurs ta siya a kasuwar musayar 'yan kwallo ta bana.

A ranar Juma'a za a gwada lafiyarsa a London.

Soldado mai shekaru 28, wanda ya bugawa tawagar 'yan kwallon kasar Spain wasanni sau 11, ya zira kwallaye 30 cikin wasanni 46 na gasar La Liga a kakar wasan da ta wuce.

A watan daya wuce, Tottenham ta sayi Paulinho daga kungiyar Corinthians ta Brazil akan fam miliyan goma sha bakwai, sannan kuma ta sayi Nacer Chadli daga FC Twente akan kusan fam miliyan bakwai.

A halin yanzu kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya ce kulab din na kokarin sayen dan wasan Tottenham Gareth Bale a kan fam miliyan tamanin.

Karin bayani