Fifa ta amince da hana Kallon yin takara

mohamed kallon
Image caption Mohamed Kallon da sauran 'yan takarar sun roki magoya bayansu ka da su tada hankali

Hukumar kwallon kafa ta duniya ta amince da hunkuncin hana Mohamed Kallon da wasu biyu takarar shugabancin hukumar kwallon kasar.

Jami'an Fifa biyu da Primo Corvaro da Prosper Abega da suka je Freetown domin sanya ido a zaben.

Ana ganin su suka tabbatar da cewa hukuncin hana takarar da kwamitin wasanni na rikon kwarya na kasar ya yi shi ne karshe.

Hakan ya kara tabbatar da cewa Isha Johansen ce kadai za a zaba ba tare da hamayya ba a zaben na ranar Asabar.

Za ta zama mace ta farko da za ta shugabanci hukumar kwallon kafa ta Saliyo.

An hana Kallon tsohon dan wasan Inter Milan da AS Monaco saboda hukumar ta ce bai zauna a kasar ba kasa da shekaru biyar kafin taron neman takarar.

Sai dai tsohon kyaftin din na Saliyo ya ce ya cancanta kuma yana da goyon bayan manyan kungiyoyin wasan kasar da suka kauracewa gasar lig din kasar akan hukuncin.

Sauran 'yan takarar biyu da aka hana tsayawa su ne Rodney Micheal da Foday Turay akan cewa suna da alaka da wani gidan caca.

Karin bayani