Liverpool ta bada tayin Deigo Costa

Image caption Diego Costa na Brazil

Liverpool ta bada tayin pan miliyon 21 a kan dan kwallon Atletico Madrid Diego Costa.

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya ce yana saran dan kwallon mai shekaru 24 zai koma kulob din.

Costa dan kasar Brazil, wanda ya koma Atletico daga kungiyar Valladolid a shekara ta 2010.

Liverpool ta ki maida martani a kan cewar siyo dan wasan zai bada damar Luis Suarez ya koma Arsenal.

Dan kwallon Uruguay din na son barin Anfield bayanda Arsenal ta bada tayin pan miliyon 40 a kansa.

Kocin Athletico Diego Simeone ya ce Costa zai iya tafiya saboda zuwa David Villa daga Barcelona.

Karin bayani