'Mun rage bai wa 'yan wasa garabasa'

Image caption Hukumar Kwallon kafa a Najeriya ta dage kan rage garabasa

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta dage kan matakinta na rage kudaden garabasar wasanni ga 'yan wasa, wato March bonus.

Rage kudaden da hukumar ta yi yunkurin yi a lokacin da 'yan wasan Najeriya za su tafi Brazil don gasar nahiyoyi ya sa sun kusa kauracewa gasar.

Ko da yake Ma'aikatar da ke kula da wasanni a Najeriya ta hada wani kwamitin bincike kan garabasar da ta jawo rashin jituwa amma Hukumar Kwallon kafar ta ce ba za ta sauya matakinta ba.

Hukumar dai za ta rage kudaden garabasar cin wasa dala dubu goma zuwa dala dubu biyar, sannan kuma za ta mayar da garabasar yin canjaras dala dubu biyu da dari biyar a maimakon dala dubu biyar.

Karin bayani