Johansen ta zama shugabar Hukumar kwallon kafa

Image caption Mace ta zama shugabar Hukumar Kwallon kafa a Saliyo

An zabi Isha Johansen a matsayin sabuwar Shugabar hukumar kwallon kafa ta Saliyo.

An dai zabe ta ba hamayya ranar Asabar bayan da 'yan takara uku da za su kara da ita aka ce basu cancanci tsayawa takarar ba.

Johansen mai shekaru 48 ta zama shugabar Hukumar kwallon kafa mace ta biyu a duniya baya ga Lydia Nsekera ta Burundi.

Babban kalubalenta na farko da ta fuskanta shi ne ta dawo da gasar kulob kulob ta League ta kasar bayan da suka kauracewa wasanni kan hana 'yan takarar shugabancin uku tsayawa takarar.

Johansen take cewa " za mu iya aiki tare domin ba ni da masaniyar komai da komai. Ina kira da a mayar da wukar."

Karin bayani