Villas-Boas ya soki Real Madrid

Image caption Andre Villas-Boas ya zargi Real Madrid

Kochiyan Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Andre Villas-Boas, ya soki kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kwakwazo kan sha'awarsu ta dan wasan nan Gareth Bale.

Kochiyan Real Madrid Carlo Ancelotti ya bayyana cewa suna tattaunawa kan sayan dan gaban Spurs mai shekaru 24.

Shi kuwa Villas-Boas cewa ya yi " rade radin da ake yi cewa komai ya kusa kankama ba gaskiya ba ne".

Villas-Boas ya kara da cewa Carlo mutun ne wanda suke mutunta juna amma kan wannan batun sun yi gaggawar bayyanawa ga jama'a.

Karin bayani