Moses ya shirya lallasa Afrika ta Kudu

Image caption Victor Moses

'Yan wasan Super Eagles na dakon zuwan ranar 14 ga watan Agusta don fafatawa da Bafana Bafana a gasar cin kofin Mandela.

Tawagar 'yan Najeriya ciki hadda Victor Moses da Obinna Nsofor da Ahmed Musa da kuma Brown Ideye sun ce za su buga wasan da za a kara da Afrika ta Kudu.

Dan wasan Chelsea, Victor Moses shi ne ya fara nuna kwadayin buga wasan.

Sai dai kuma Spartak Moscow ta ce ba za ta bar dan wasanta Emmanuel Emenike yazo ya bugawa Najeriya kwallon ba.

Najeriya za tayi amfani da wasan don shiryawa fafatawar da za tayi da kasar Malawi a watan Satumba na share fagen buga gasar cin kofin kwallon duniya ba za ayi a Brazil a shekara ta 2014.

Karin bayani