Newcastle ta karbi aron Loic Remy

Image caption Loic Remy

Newcastle ta sayi dan wasan Queens Park Rangers, Loic Remy a matsayin aro na kakar wasa daya.

Dan kwallon mai shekaru 26 a watan Junairu yaki amincewa da Newcastle din inda ya koma QPR daga kungiyar Marseille ta Faransa.

Remy ya bayyana cewar "Na ji dadin komawa wannan kulob din".

Ya kara da cewar "abin alfahari ne kulob din da yayi zawarci na a watan Junairu, ya kara nuna sha'awarsa a kaina".

Dan kwallon Faransa ya koma QPR a kan pan miliyon takwas a farkon bana.

Ya zira kwallaye shida a tawagar Harry Redknapp amma duk da haka ta nutse daga gasar Premiership zuwa Championship.