Rooney na bukatar tilasta tafiyarsa

wayne rooney
Image caption Ince na ganin bayan shekaru tara da nasarar daukar kofuna Rooney na bukatar sauyi

Tsohon dan wasan Manchester United Paul Ince ya ce in har Wayne Rooney na son barin kungiyar sai ya tilasta wa klub din.

Kociyan na Black Pool a yanzu ya ce abu ya rage ga Rooney idan yana son tafiya to sai ya tashi tsaye ya bukaci hakan.

Man United ta kara cewa dan wasan ba na sayarwa ba ne bayan ta ki tayi na biyu da Chelsea ta yi na fam miliyan 25 a kan sa.

Rooney mai shekara 27 ba ya daga cikin wadanda za su yi wa kungiyar wasa ranar Talatar nan da Stockholm sabo da rauni a kafadarsa.

Karin bayani