Gwanar Olympics ta yi murabus

beth tweddle
Image caption Duk da ciwon guiwar da tai fama da shi Beth Tweddle ta ci gaba da zama gwarzuwa a wasan

'Yar wasan tsalle-tsalle da ta fi samun lambobin Olympics a Birtaniya Beth Tweddle ta yi murabus.

Tweddle mai shekaru 28 ta sanar da ritayar ne a zagayowar ranar da ta samu lambar tagulla a gasar Olympics ta London 2012.

Tana shekara 17 ta fara cin lambobin gasa a wasan Commonwealth a Manchester inda ta samu zinare da azurfa biyu.

A shekarun da suka biyo baya ta yi nasarar samun lambobin zinare sama da 20 a manyan wasanni na duniya.

Karin bayani