Barcelona ta nemi David Luiz

David Luiz da rafeal
Image caption David Luiz ya taba sa alkalin wasa ya kori Rafeal a lokacin karawar Man United da Chelsea

Barcelona ta gabatar wa Chelsea bukatar sayen dan wasanta na baya dan Brazil David Luiz.

Barcelona ta dade tana harin Luiz mai shekaru 26 da ya koma Chelsea daga Benfica akan kusan fam miliyan 21 a watan Janairu na 2011.

Sai dai Chelsea tun a baya ta nanata cewa dan wasan da ya yi mata wasa sama da dari daya ba na sayarwa ba ne.

Ana ganin tayin na Barcelona na kudi ne kawai ba tare da musayar wani dan wasa ba.

Barcelona tana matukar bukatar dan wasan baya saboda Carles Puyol yana jiyya sauran su Gerard Pique da Adriano Correia da Javier Mascherano ko dai sun ji ciwo ko an dakatar da su a bara.

Karin bayani