Alkali ya tsayar da wasa saboda buda baki

Image caption Kwallon kafa

Wani abinda ba kasafai ake ganin irinsa ba, ya faru a kasar Senegal inda alkalin wasa ya dakatar da wasan kwallon kafa don ya sha ruwa saboda azumi.

Ana fafatawa a wasa tsakanin Casa Sport da Yeggo, kwatsam sai alkalin wasa Ousseynou Gueye ya dakatar da wasan, ya je gefen fili yayi buda baki da dabino da ruwa.

Matakin ya harzuka 'yan kwallo inda suka yi ta ihu, amma ko a jikinsa, har sai da ya cika cikinsa kafin a ci gaba da wasan.

Alkalin wasan Gueye ya ce " a ka'ida ba dai-dai ba ne a tsayar da wasa don asha ruwa, amma kuma jiki da jini".

Karin bayani