Liverpool ku barni in tafi - Suarez

Image caption Luis Suraez

Luis Suarez ya ce yanason ya bar Liverpool ya koma kungiyar da za ta fafata a gasar zakarun Turai.

Dan kwallon Uruguay mai shekaru 26, na shirin mika takardar neman izinin barin kulob din a karshen mako.

Suarez ya bayyanawa jaridu biyu na Birtaniya wato Guardian da Daily Telegraph cewar Liverpool ta yi masa "alkawarin" zai iya tafiya idan har bata tsallake zuwa gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa ba.

"Na sadaukar da kai a kakar wasan data wuce. Yanzu lokaci yayi da Liverpool za ta mutunta yarjejeniyarmu", in ji Suarez.

Arsenal ta bada tayin dan kwallon har sau biyu, amma Liverpool ta ki amincewa.

Karin bayani