Emenike ya kara komawa Fenerbahce

Image caption Emmanuel Emenike

Emmanuel Emenike ya bayyana gamsuwarsa ta komawa kungiyar Fenerbahce ta Turkiya daga Spartak Moscow a kan dala miliyon goma sha bakwai da dubu dari hudu.

Dan Najeriyar mai shekaru ashirin da shida, ya kara komawa kulob dinne bayan shafe shekaru biyu yana taka leda a Rasha.

Emenike yace "lokacin da aka soma maganar in koma, sai nace Allah yasa kungiyoyin biyu su daidai ta".

A ranar Alhamis aka gwada lafiyar Emenike a Istanbul kuma nan da 'yan kwanaki zai sanya hannu a yarjejeniya da kulob din.

Da farko Emenike ya koma Fenerbahce a watan Mayun shekara ta 2011 daga kungiyar Karabukspor amma sai ya bar kulob din ba tare da buga wasa ko guda ba.

Karin bayani