Usain Bolt ya sake nasara

usain bolt
Image caption Usain Bolt ya ce, '' ina farin ciki amma na so in fi haka''

Zakaran tseren mita 100 na wasan Olympics Usain Bolt ya sake karbe lambar zinariya ta tseren a Moscow.

Usain Bolt dan Jamaica ya yi nasarar ne a gasar wasannin motsa jiki ta duniya a Moscow.

Inda ya yi nasarar kammala tseren cikin dakika 9.77.

Bolt mai shekara 26 da sau shida yana daukar lambar zinariya a tseren ya kasa ba Amurke Justin Gatlin.

Gatlin wanda ya zo na biyu ya samu lambar azurfa ya kammala tseren cikin dakika 9.85.

Nesta Carter dan Jamaica shi ma ya zo na uku cikin dakika 9.95.