Kofin Duniya: Sai dai Premier ta hakura

sepp blatter
Image caption Fifa ba ta yi la'akari da tsananin zafin Qatar ba lokacin da ta bai wa kasar damar gudanar da gasar a 2010.

Mataimakin shugaban Fifa Jim Boyce ya ce kila sai Premier ta hakura da sauyin gasar Kofin Duniya na 2022.

Shugaban Fifa Blatter yana son matsar da gasar da za a yi a Qatar zuwa lokacin sanyi saboda zafi a lokacin da a ka tsara yin ta.

Hukumomin gasar Premier suna adawa da hakan da cewa zai rikita tsarinsu.

Jim Boyce ya ce ya fahimci matsayin 'yan Premier amma kuma magana ce ta shekara 9.

Ba abu ne da za a yi a shekara mai zuwa ko shekara ta gaba ba.

Ya ce, a don haka yana fatan hukumomin Premier za su zauna su duba tsarin.

Karin bayani