Moyes ya musanta sabani da Rooney

wayne rooney
Image caption Rooney na son barin Man United bayan shekara tara da ya dawo daga Everton

Mai horad da 'yan wasan Manchester United David Moyes ya musanta rahotannin da ke cewa ya yi watsi da Wayne Rooney.

Rooney wanda ya ji rauni a kafadarsa da kuma Chelsea ke nema bai buga wasansu da Wigan ba na Community Shield.

Moyes ya ce ko alama bai saba da Rooney ba, wanda ya ce yana atisaye da 'yan wasansu na ko-ta-kwana kamar yadda ya bukata da kansa.

Kociyan ya ce yana jin dadin maganar da a ke yi a kan Rooney.

Ya ce, ''da dama daga cikinku ba ku fahimci maganar ba. Ba za a sayar da shi ba.''

Duk da rashin buga wasansu da Wigan, kocin Ingila Roy Hodgson ya zabe shi ya buga wa Ingila

wasan sada zumunta da Scotland ranar Laraba.

Karin bayani