Ohuruogu ta kafa tarihi

christine ohuruogu
Image caption Christine Ohuruogu ta ce ta yi mamakin wannan nasara tata, abin kamar mafarki

Christine Ohuruogu ta zama 'yar Birtania ta farko da ta samu lambobin zinariya a Gasar Wasanni ta Duniya.

Mai shekaru 29 Ohuruogu ta yi wannan bajinta ne bayan da ta zama ta farko a tseren mita 400.

'Yar tseren 'yar asalin Najeriya ta kuma kawar da bajintar tarihi a Birtaniya ta Kathy Cooke.

Ohuruogu ta yi galaba ne a kan mai rike da kambun gasar Amantle Montsho 'yar Botswana.

Dan bambamcin lokaci kalilan a ka samu tsakanin 'yan tseren biyu.

'Yar Rasha Antonina Krivoshapka ita ce ta samu lambar tagulla.

A shekara ta 2007 Ohuruogu ce ta zama ta daya a Gasar.

Ita ce kuma ta samu lambar zinariya ta gasar Olympics shekara daya baya.