Ko da yaushe zan gayyaci Rooney: Hodgson

wayne rooney
Image caption Sau 83 Rooney ya yi wa Ingila wasa ya ci kwallaye 36

Kociyan Ingila Roy Hodgson ya ce yana fatan Wayne Rooney zai manta da rigimar da ke tsakaninsa da Man United ya mayar da hankalinsa kan wasan Ingila da Scotland.

A ranar Laraba ne Ingila za ta yi wasan sada zumunta da Scotland a shirin da ta ke na tunkarar wasanninta na neman zuwa Gasar Kofin Duniya.

A wata mai zuwa Ingila za ta kara da Moldova da Ukraine don neman zuwa Gasar Kofin Duniya.

Ingila ce ta biyu a rukuninsu da maki biyu bayan Montenegro.

Hodgson ya ce komai halin da Rooney ke ciki da kungiyarsa za a gayyace ya yi wa kasarsa wasa saboda yana daya daga cikin gwanayenta.

Kociyan ya ce Rooney, '' ba ya tare da wata damuwa kuma zai iya yi wa kungiyarsa wasa da kuma kasarsa, abin da na ke tsammani daga duk wani dan wasa.''

Hodgson ya ce kungiya da kasa daban su ke, 'yan wasa ba za su kawo matsalolinsu na klub kungiyar kasa ba, haka kuma ba za su dauki matsalarsu ta kungiyar kasa su kai klub ba.

Kociyan ya kara da cewa ,''ina tsammanin duk dan wasan da ya zo nan ya mayar da hankalinsa a kan yi wa Ingila wasa kawai.''

Karin bayani