Bale ba ya cikin tsarina - Ancelotti

gareth bale
Image caption Bale ba zai buga wa Wales wasan sada zumunta da Jamhuriyar Ireland ba ranar Laraba

Kociyan Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce Gareth Bale baya daga cikin tsarinsa a kakar wasannin da za a shiga.

Mai horad da 'yan wasan ya sheda wa shugaban kungiyar ne Florentino Perez hakan.

Ana ganin kalaman na Ancelotti sun biyo bayan kin sanya hannu da Ronaldo yayi kan sabunta zamansa a klub din a bainar jama'a a makon da ya wuce.

Da kuma yadda magoya bayan kungiyar a Madrid suka sauya ra'ayinsu akan dan wasan na Tottenham.

Magoya baya da 'yan wasan kungiyar suna ganin babu dalilin da zai sa a sayi Bale akan sama da fam miliyan 60.

Sauyin matsayin na Real Madrid ana ganin zai sa Man United ta gabatar da bukatarta ta sayen Bale.

Kociyan United David Moyes da ke sha'awar Bale na dari-darin neman sa saboda rashin niyyar Tottenham ta sayar da shi.

Da kuma alamun rashin sha'awar shi kansa dan wasan ta son komawa Old Trafford.

Karin bayani