Downing ya koma West Ham

stewart downing
Image caption Stewart ya yi kungiyoyin Middlesbrough da Sunderland da Aston Villa kafin Liverpool

Kungiyar West Ham ta sayi Stewart Downing na Liverpool akan kusa da fam miliyan biyar.

Downing mai shekara 29 da ke yi wa Ingila wasa ya kulla kwantiragin shekaru hudu da West Ham.

Da wannan shi ma ya bi Andy Carroll da ya bar Liverpool din zuwa Upton Park.

A shekara ta 2011 ne Liverpool ta sayo Downing daga Aston Villa akan fam miliyan 20.

Sau 34 Downing yana yi wa Ingila wasa kuma sau tara ya ci wa Liverpool kwallo a wasanni 91 da ya yi mata gaba daya.

Shi kuwa Carrol Liverpool ta sayo shi ne a kan fam miliyan 35 a watan Janairu na 201.

Kuma West Ham ta saye shi a farkon bazaran nan bayan ya yi zaman aro na kakar wasanni daya a kungiyar.

Karin bayani