Mo Farah na gab da kafa tarihi

mo farah
Image caption Farah ya ce yayi nawa a tseren kusa da karshe domin ya iya fuskantar wasan karshen da karfinsa

Fatan Mo Farah na kara lambobin zinare na gudun mita 5,000 da 10,000 akan wadanda ya samu a Olympics ya karu.

Dan tseren na Birtaniya dan asalin Somalia na gab da wannan bajinta ne bayan da kai wasan karshe na gudun 5,000 a gasar wasannin Duniya da ake yi a Moscow.

Farah da ke rike da kambun gasar shi ne na biyar a jerin wadanda suka kai wasan na kusa da karshe, wanda wannan ne maki na karshe da ake zabar wadanda za su fafata a karshe.

Idan ya yi nasara a fafatawar ta karshe ranar Juma'a, Farah zai bi sahun Kenenisa Bekele na Ethiopia.

Ya zama mutum na byu da ya yi nasarar gudun mita 10,000 da 5,000 na Olympics da kuma na Gasar Duniya.

Farah mai shekara 30 ya ci lambobin zinare a tseren biyu a wasan Olympics na London 2012.

Kuma ranar Asabar ya zama dan Birtania na farko da ya yi nasara a gudun mita 10,000 a Gasar Duniya.

Karin bayani