Gabriel zai koma fagen tamaula

Reuben Gabriel
Image caption Mai horar da 'yan wasan Najeriya, Stephen Keshi ya yi murna da komowar Gabriel fagen tamaula

Dan wasan tsakiyar nan na Najeriya, Reuben Gabriel ya bayyana takaicin da ya ji na rashin buga kwallo a tsawon watanni uku.

Dan wasan mai shekaru 22 a yanzu ya samu damar yin cikakken horo da kulob din Kilmarnock na Scotland, bayan an yi masa aiki a kasan mararsa.

Gabriel ya shaida wa BBC cewa "Abin bacin ran ma shi ne kallon sauran 'yan wasan kungiyar Scotland da abokan wasa na a lokacin da suke wasa."

"Ina jin bakin cikin rashin kasancewa tare da su, amma bani da wani zabi, domin abin da zan yi kawai shi ne na maida hankali na ga na samu cikakkiyar lafiya a tsawon kusan watanni uku"

Tsohon dan wasan tsakiyar na Kano Pillars, kuma dan wasan kungiyar Super Eagles ya kamu da karambau abin da ya sa aka hana shi wasa.

Kuma watanni biyu bayan samun nasarar Super Eagles a Afrika ta Kudu ne, Gabriel ya koma kulob din Kilmarnock tare da Papa Idris.

"Ba na iya zama na mintoci biyar ba tare da na yi tunanin taka leda ba, saboda haka abun takaici ne, amma yanzu duk wannan ya wuce." Inji Gabriel.