Najeriya ta dauki Kofin Mandela

stephen keshi
Image caption Keshi ya jagoranci Najeriya ta yi nasara akan Afrika ta Kudu a karo na shida

A wasannin sada zumunta na kwallon kafa da aka yi tsakanin kasashe daban-daban, Najeriya ta ci Afrika ta Kudu 2-0, Brazil kuma ta sha kashi.

Nasarar ta bai wa Najeriya damar daukar Kofin Mandela na wasan sada zumunta.

A wasan Najeriyar Uche Nsofor shi ne ya ci kwallayen biyu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Wannan shi ne karo na shida da Najeriya take nasara a haduwarta da Afrika ta Kudu takwas.

Ruwanda ta sha kashi 1-0 da Malawi,Turkiyya da Ghana sun tashi 2-2, Masar ta ci Uganda 3-0, Chile 6-0 Iraq.

Switzerland ta ci Brazil 1-0, Jamus da Paraguay 3-3, Italiya ta sha kashi 2-1 da Argentina.

Belgium da Faransa 0-0, Poland ta ci Denmark 3-2, Sweden ta ci Norway 4-2, Romania da Slovakia 1-1.

Algeria da Guinea sun tashi canjaras 2-2, yayin da Ireland ta Arewa ta ci Rasha a wasan neman zuwa gasar Kofin Duniya.