Barcelona ce sanadin rashin lafiyar Neymar —Scolari

neymar
Image caption Ina ganin wadannan da suka san komai(Barcelona)suke ganin ko da yaushe daidai suke su suka haddasa masa inji Scolari

Kociyan Brazil Luiz Felipe Scolari ya yi kakkausan suka ga Barcelona akan kula da Neymar kuma ya dora alhakin rashin lafiyar dan wasan a kanta.

A farkon watan nan ne aka gano dan wasan mai shekaru 21 ya kamu da fara (cutar karancin jini) bayan da aka yi masa aikin fitar da beli a watan Yuli.

Scolari yayi kakkausan suka ga Barcelonan saboda bai wa dan wasan shawarar a yi masa tiyatar da yadda suke kula da shi tun da ya koma can.

Scolari ya ce ba abu ne da za a yarda cewa Neymar ya kamu da fara ba.

Ya ce Neymar na tare da Barcelona kafin gasar Zakarun Nahiyoyi kuma lafiyarsa kalau a lokacin, amma a yanzu a fili take ba kamar da ya ke ba.

A farkon bazaran nan Neymar ya koma Barcelona daga Santos akan euro miliyan 57 kuma an ce ya rage nauyi da kilogram bakwai tun bayan da aka yi masa tiyata.

Karin bayani