Ameobi na son wasa akai-akai saboda Najeriya

shola ameobi
Image caption Shola ya fara buga wa Newcastle wasan Premier a karawarta da Chelsea a Satumba na 2000

Shola Ameobi na son Newcastle ta rika sa shi a wasa sosai domin samun damar buga wa Najeriya yadda ya kamata a gasar Kofin Duniya.

Duk da cewa ya buga wa kungiyar matasa ta Ingila wasa sau 20 sauya dokokin Fifa da aka yi ya bai wa dan wasan haifaffen garin Zaria damar buga wa najeriya wasa.

Mai shekaru 31 wanda sau daya ya taba yi wa Najeriya wasa sau hudu kawai ya yi wasan Premier a kakar da ta wuce.

Dan wasan ya ce,'' shekaru da dama ban iya yi wa Najeriya wasa ba amma Fifa ta sauya dokokinta yanzu, ina da damar yin abin da kowana dan wasa ke fata, shi ne wasa a gasar Kofin Duniya.

Ameobi ya cancanci buga wa Najeriya wasa saboda yana da takardar zama dan kasashe biyu, Najeriya da Ingila kuma bai taba yi wa kungiyar wasan Ingila ta manya wasa ba.

Karin bayani