Bartolli za ta yi ritaya daga tennis

Image caption Marion Bartolli

Tauraruwar gasar Wimbledon a tennis 'yar kasar Faransa, Marion Bartolli ta ce za ta yi ritaya daga buga wasan tennis.

Bartolli wacce ita ce ta bakwai a fagen tennis na mata a duniya, ta dauki matakin ba za ta na daina wasa, inda ta fashe da kuka.

Matakinta ya biyo bayan jinyar raunuka da take ta fama dasu.

'Yar shekaru ashirin da takwas, Bartolli ta taka muhimmiyar rawa a fagen tennis a duniya.

Manyan 'yan wasan tennis a duniya, sun jinjinawa Bartolli a matsayin hazika wacce ta taimaka wajen habbaka wasa tennis a tsakanin mata a duniya.

Karin bayani