Tottenham ta sayi Etienne Capoue

etienne capoue
Image caption Zuwansa Tottenham zai bai wa wani dan wasan tsakiya damar barin kungiyar

Tottenham ta sayi dan wasan tsakiya na Faransa Etienne Capoue daga kungiyar Toulouse ta Faransan.

Dan wasan mai shekara 25 da ake ganin cinikin nasa ya kai fam miliyan tara shi ne na hudu da Tottenham ta saya a wannan lokacin na musayar 'yan wasa.

Capoue wanda ya buga wa Toulouse wasa sau 174 ya ci kwallaye 13, sau bakwai ya yi wa Faransa wasa kuma yana iya wasa a matsayin dan baya.

Yana daga cikin gwanayen 'yan wasan da aka zaba da suka yi fice na shekara ta 2012 a Faransa hadi da mai tsaron gidan Tottenham Hugo Lloris.

Capoue ya bi layin dan wasan Brazil Paulino da dan Belgium Nacer Chadli da dan Spaniya Roberto Soldado wajen dawo wa Tottenham din.

Karin bayani