Kalaman Malawi sun harzuka Keshi

stephen keshi
Image caption Keshi ya ce,'' ku gaya masa a Calabar za a yi wasan in ya ga dama ka da ya zo''

Kociyan Najeriya Stephen Keshi ya maida martani ga hukumar kwallon kafa ta Malawi akan bukatarta ta sauya filin wasansu da Najeriyar na neman zuwa gasar Kofin Duniya.

Hukumar ta Malawi ta rubuta wa Fifa takarda tana bukatar ta sa a sauya wurin wasan da zai tabbatar da wadda zata fito a rukunin na 6 Group F, daga Calabar.

Kuma Kociyan 'yan Malawin Tom Saintfiet a makon da ya wuce ya ce hankalinsa bai kwanta ba da birnin na Calabar saboda yana fargabar rashin tsaro.

Akan hakan ne kociyan na Najeriya da ke gaban Malawin da maki biyu a rukunin ya ce ba za a sauya filin wasan ba saboda takwaran nasa ba shi da ikon tsara wa Najeriya inda za ta yi wasanta.

Akan bukatar ta Malawin ne Fifa ta nemi Najeriya ta bata bayanin irin matakan tsaron da ta shirya wa wasan da za a yi ranar 7 ga watan Satumba.

Wasan shi ne zai tabbatar da kasar da zata je mataki na gaba na kasashe goma da za a fitar da guda biyar da za su wakilci Afrika a gasar Kofin Duniya da za a yi a Brazil a shekara mai zuwa.

Karin bayani