Arteta zai yi jinyar makwanni shida

Image caption Mikel Arteta

Dan wasan Arsenal Mikel Arteta zai shafe makwanni shida yana jinya saboda rauni a kafarsa.

Dan kasar Spain mai shekaru talatin da daya, ya samu rauni lokacin horo, sannan kuma kocinsa Arsene Wenger bai bayyana tsananin raunin ba.

Wasu 'yan Arsenal, Thomas Vermaelen da Nacho Monreal suma suna fama da rauni kuma ba za su buga wasan bude gasar tsakaninsu da Aston Villa ba.

Sai dai bisa dukkan alamu Theo Walcott da Aaron Ramsey za su murmure don karawar ta farko a ranar Asabar.

Arsenal na fuskantar matsala saboda galibin manyan 'yan wasanta ba su da koshin lafiya.

Karin bayani