Bale zai yi jinyar makwanni biyu

Image caption Gareth Bale

Kocin Tottenham, Andre Villas-Boas ya bayyana cewar dan wasansa, Gareth Bale zai yi jinyar makwanni biyu.

Bale mai shekaru 24, wanda ake ta alakanta shi da komawa Real Madrid, ba zai buga wasansu na farko ba da Crystal Palace a ranar Lahadi saboda rauni.

Spurs za ta hadu da Dinamo Tbilisi a gasar Europa League a ranar Lahadi kafin ta fafata da Swansea kwanaki uku.

Idan har Bale ya koma taka leda a cikin makwanni biyu masu zuwa, tabbas zai iya buga wasan Spurs da Arsenal da za su kara a Emirates a ranar daya ga watan Satumba.

Akwai rahotannin dake nuna cewar Real Madrid za ta kulla yarjejeniya da dan wasan na kasar Wales a kan pan miliyon tamanin.

Karin bayani