Wenger ya bawa 'yan kallo hakuri

Image caption Wenger na rarrashin masu son kulob din Arsenal

Mai bada horo na Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger ya nemi afuwa ga masu marawa kulob din baya.

Arsene Wenger ya nemi afuwar ne bayan da a wasan farko a gasar Premier League Aston Villa ta lalla sa su da ci uku da daya.

An dai ta yiwa 'yan wasan Arsene Wenger ihu a karshen wasan.

Anyi ta korafi kan dan kasar Faransar da ya kara kaimin karfafa tawagarsa kafin a rufe sayan 'yan wasa ranar biyu ga watan Satumba.

An ambato shugaba mai cikakken iko na kulob din, Ivan Gazidis na cewa Arsenal za ta kashe kudade makudai amma dan wasa daya ne kawai Yaya Sanogo ya isa ga kulob din.

Karin bayani