2022: Zafin Qatar na jan hankali

Image caption 2022: Zafin Qatar ya sa an fara tunanin saukar bakin ta

Tsohon shugaban kungiyar kwallon kafa, David Bernstein, ya ce ya kamata a sake sabon lale kan zabar masu saukar baki na gasar cin kofin duniya na shekara ta dubu biyu da ashirin da biyu da za a yi a Qatar; maimakon a sauya lokaci.

Ana nuna damuwa akan zafin da ake yi a Qatar a lokacin bazara, in da hasashe ke nuna yanayin na iya kaiwa maki hamsin na ma'aunin shelsiyos.

Mr Bernstein, ya ce a ganin sa ko dai a bar shi kamar yadda aka tsara ko kuma a sake sabon lale.

Qatar dai ta samu nasarar zama mai masaukin bakin gasar cin kofin duniya a shekara ta dubu biyu da ashirin da biyu ne bayan da ta doke Afrika ta kudu da Korea da Japan da Australia da kuma Amurka.

Karin bayani