United na zawarcin Fellaini da Baines

Image caption Fellaini and Baines

Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta ki amincewa da tayin fan miliyon 28 da Manchester United ta bayar don sayen Marouane Fellaini da kuma Leighton Baines.

Tsohon kocin Everton David Moyes ya bada tayin fan miliyon 16 a kan Fellaini sai kuma fan miliyon 12 a kan Baines.

'Yan wasan biyu sun buga wa Everton a wasanta na ranar Asabar da suka tashi biyu da biyu tsakaninsu da Norwich.

Moyes shi ne ya siyo 'yan wasan biyu lokacin yana Everton, wato Baines daga Wigan a kan fan miliyon shida a watan Agustan 2007 sai kuma Fellaini daga Standard Liege a watan Satumbar shekara ta 2008.

Karin bayani