Manchester City ta hau tebur

manchester city ta ci newcsatle
Image caption Man city ce ta fi kashe kudi wajen sayen 'yan wasa a bana da kusan fam miliyan 87 akan 'yan wasa hudu

Manchester City ta zama ta daya a tebur din Premier bayan ta ci Newcastle 4-0 a wasansu na farko na gasar.

David Silva ne ya fara daga raga a minti shida da wasa bayan da Edin Dzeko ya kwararo wata kwallo ta gefe.

Sai kuma Sergio Aguero ya biyo baya da kwallo ta biyu a minti na 22 kafin a alkalin wasa ya kori Steven Taylor na Newcastle kan laifin da ya aikata akan Aguero.

Yaya Toure ne ya ci kwallo ta uku a bugun tazara bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 50.

Can kuma a minti na 75 Samir Nasri ya rufe cin da kwallo ta hudu wadda ta tabbatar wa Manchester City nasarar zama ta daya a wasanta na farko.

Da maki 3 kamar sauran kungiyoyi tara na farko daga cikin su ashirin amma kuma da bambamcin kwallaye 4.

Manchester United ta na ta biyu da bambancin kwallaye 3, sai Aston Villa mai kwallaye 2, Chelsea kuma na bin baya ita ma da bambamcin kwallaye 2.

Newcastle ta karshe wato ta ashirin da aka jefa mata kwallaye hudu a raga ba tare da ta sa ko da daya ba.

Karin bayani